Sabbin dokokin yaki da ta'adanci a Birtaniya

David Cameron Hakkin mallakar hoto
Image caption David Cameron

Gwamnatin Birtaniya na duba yuwuwar bullo da wani tsari na wucin-gadi na hana 'yan kasar da ake zargi sun je sun taimaka wa kungiyoyin 'yan gwagwarmaya yaki a kasashen waje, dawo wa kasar.

Wasu kafofin gwamnati sun sheda wa BBC cewa a yau Litinin, Fraiminista David Cameron na shirin bayyana wasu matakai, na kalubalantar barazanar masu da'awar kafa daular musulunci.

Sai dai 'yan jam'iyyar Liberal Democrats sun damuwa a kan wannan mataki da zai kai ga kwace fasfuna da hana shiga kasar na wucin gadi.

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ta masu matsakaicin ra'ayin suna shakkun halarcin matakan ta fannin shari'a.