Nigeria ta warware matsalar visa da Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Miliyoyin jama'a na gudanar aikin hajji a duk shekara

Hukumar kula da aikin hajjin Nigeria ta ce a yanzu haka an warware matsalar da ke tsakaninta da ofishin jakadancin Saudiyya game da bayar da visa domin fara aikin hajjin bana.

A da hukumar alhazan ta koka cewa ana samun jinkirin samun visa bayan da ta ce za ta fara jigilar alhazai nan da kasa da mako guda.

"Wannan matsala an magance ta, dama tangarda ce aka samu daga na'urar Saudiyya", In ji Kakakin hukumar alhazan, Alhaji Uba Mana.

Ya kuma kara da cewa tuni aka fara tantance fasfunan mahajjatan jihohin Kano da Jigawa da Sokoto da kuma Yobe.

Kasar Saudiyya ta haramtawa kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia zuwa aikin hajjin bana saboda bullar cutar Ebola.

Karin bayani