Ana cigaba da zanga zanga a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana cigaba da fada tsakanin masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da jami'an 'yan sanda a gaban zauren Majalisar dokokin kasar Pakistan a Islamabad, babban birnin kasar.

Wakilin BBC ya ce wasu magoya bayan dan siyasan nan mai adawa,Imran Khan da kuma fitaccen malamin nan,Tahir ul-Qadri sun cinna wa wasu kwantainoni wuta.

Haka kuma suna cigaba da dannawa cikin gine-ginen gwamnati, abin da ya tilasta wa 'yan sanda ja da baya.

Masu zanga-zangar suna bukatar Fraiminista Nawaz Sharif ya yi murabus ne.

Rikicin ya barke ne a ranar Asabar, bayan 'yan kwanaki ana zanga-zangar lumana.