Ana taro kan Boko Haram a Abuja

Image caption Wakilan kasashen da ke halartar taron a Abuja

Yanzu haka dai Abuja babban birnin Nigeria na karbar taron ministocin harkokin waje na wasu kasashen duniya kan tsaro a kasar.

Taron dai na bitar batutuwan da aka tattauna ne a yayin tarukka koli da aka yi a biranen Paris da London da kuma Washington inda aka tabo batutuwan da suka shafi tsaro a kasar - wato tayar da kayan bayan kungiyar Boko Haram.

Ministan harkokin wajen Nigeria, Ambasada Aminu Wali shi ne ya yi jawabin maraba a taron.

Wali yace " Wannan taron ya Samar da wata dama ta yin bitar da cika ken nazari kan yadda aka aiwatar da abubuwa da aka cimma a tattauna war da aka yi wajen wadannan tarukan ciki kuwa har da girman tai makon da kasashen duniya suka ba Nigeria da kuma kokarin ita kanta gwamnatin Nigeria ke yi wajen yaki da kungiyar Boko Haram".

" Tun taron da aka yi birnin Paris, 'yan matan Chibok na ci gaba da zama hannun Boko Haram, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da suka so kuma a lokacin da suke so. Akwai bukatar mu gano wane mataki ke aiki da me muke bukatar kara yi domin kawo karshen wannan bala'in kwata-kwata'', in ji Ambasada Aminu Wali.

Wadanda aka gayyato domin halartar taron dai sun hada da ministocin hakokin waje na kasashen Benin da Kamaru da Chadi da Kuma Nijar.

Akwai kuma ministoci daga kasashen Burtaniyada Faransa da Amurka da Canada da kuma China.

Haka ma akwai wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar Ecowas da ta Tarayyar Afrika da kuma kungiyar kasashen Musulmi ta OIC.