'A mika Sherrif da Ihejirika ICC'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane, yayin da wasu dubun-dubata suka rasa matsugunansu

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta bukaci Shugaban Kasar Goodluck Jonathan da ya gaggauta mika wasu fitattaun 'yan kasar biyu ga kotun hukunta laifukan yaki na ICC.

Hakan ya biyo bayan wani zargi da wani mai shiga tsakani na gwamnatin kasar ya yi na cewa tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sherif da tsohon hafsan soji da Azubuke Ihejirika da tallafa wa kungiyar Boko Haram.

A wani taron manema labarai da jam'iyyar ta APC ta kira a Abuja ta ce dole ne shugaba Jonathan ya mika mutanen biyu domin su fuskanci tuhuma kan zargin sa hannu a rikicin Boko Haram.

Sanata Ali Modu Sherriff wanda ake kira SAS kwanan nan ya sauya sheka daga jam'iyyar APC ya koma PDP.

Tuni dai mutanen biyu suka musanta zarge-zargen da ake musu na daukar nauyin Boko Haram.