'Wuraren da Boko Haram ta kwace'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garuruwan da bisa dukkan alamu ke karkashin Boko Haram

Rahotannin da ke fitowa daga yankin arewa maso gabashin Nigeria na nuna cewar kungiyar Boko Haram na ci gaba da kwace iko da garuruwan da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Kamaru.

Tun daga farkon watan Agusta rahotannin da BBC ke samu daga mazauna garuruwa da wasu kauyuka a jihar Borno ke nuna cewar 'yan Boko Haram suke da iko da garuruwa da dama a yankin.

Gari na baya-bayanan shi ne Bama inda bayanai suka nuna cewar 'yan Boko Haram sun ci karfin jami'an tsaro sannan suka kwace garin.

Lamarin ya tilasta wa dubban mazauna Bama ficewa zuwa Maiduguri da wasu garuruwan a jihar ta Borno.

Wasu rahotannin sun nuna cewa a yanzu haka Boko Haram ne ke iko da garuruwan Gwoza da Limankara da Dikwa da Damboa da Gamborou Ngala, da Buni Yadi a jihar Yobe, da Madagali a jihar Adamawa.

Jami'an tsaron Nigeria sun ki fitowa fili su bayyana garuruwa da suka kubuce daga hannunsu, amma dai sun bayyana cewar ba za su bar wasu yankunan kasar su koma hannun 'yan Boko Haram ba.