'Har yanzu babu duriyar 'yan matan Chibok'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen 'yan matan Chibok suna cikin damuwa

Kungiyar da ke fafutukar kwato 'yan matan Chibok da aka sace, 'Bring Back Our Girls', ta ci gaba da gangami domin kara matsin lamba ga gwamnatin Nigeria ta gaggauta ceto 'yan matan.

Kwanaki fiye da 140 kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan matan sakandaren garin Chibok da ke jihar Borno kuma kawo yanzu babu duriyarsu.

Kungiyar ta 'Bring Back Our Girls' ta shafe watanni tana gudanar da tarurruka domin ganin gwamnatin Nigeria ta zage damtse a yunkurinta na kubutar da 'yan matan Chibok.

Kasashen duniya da dama sun yi alkawarin tallafawa Nigeria domin a gano inda 'yan matan suke sannan a kubutar da su da ransu, amma kawo yanzu an kasa cimma buri.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce ba za su sako 'yan matan Chibok ba har sai an sako mayakansu da ke hannun jami'an tsaron Nigeria.

Masu sharhi na ganin cewar gwamnatin Nigeria ta gaza a kokarinta na kubutar da 'yan matan a yayinda gwamnatin ke cewar tana iyaka kokarinta domin ceto su.