Dole Iran ta rungumi Internet.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto isna
Image caption Hassan Rouhani ya zama shugaban kasar Iran ne shekarar 2013.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yace dole ne malaman addini a kasar su rungumi Internet da sauran fasahohin zamani.

A wani jawabi da aka yada a gidan Talabijin na kasar, Mr Rohani yace ya na da matukar muhimmanci yaran da suke tasowa su samu damar amfani da Internet.

Shugaban wanda aka zaba a shekarar da ta gabata, ya ci alwashin ba goyon bayan yancin fadar albarkacin baki na 'yan jarida sai dai ya fuskanci adawa akan wannan batu.

A makon da ya gabata wani sanannen malamin addini a Iran Ayatollah Makarem Shirazi yace shiga Internet ta hanyar wayoyin salula bai dace ba.

Wasu malamai ma sun yi kakkausar suka kan haka, inda suka ce Internet na bada damar yada hotunan da ba su dace ba cikin sauki.

A makwannin da suka gabata dai gwamnatin Shugaba Hassan Rouhani ta bada layin Internet na 3G ga wasu kamfanonin sadarwa guda 3 a kasar, sai dai kwararru na cewa har yanzu layukan Internet din ba su da karfi a kasar.

Da yake yin wani jawabi a ranar litinin 1 ga watan Satumbar shekarar nan, Hassan Rouhani y jaddada cewar yace ya na da matukar muhimmanci yin amfani da shafin na Internet, inda yace ''Bai kamata mu hana yara masu tasowa yin alaka da sauran kasashen duniya ba''.

Mr Rouhani ya kara da cewa '' Idan har ba mu matsa zuwa sabuwar duniyar yanar gizo ta wayar salulaba a yau ba, to kuwa za mu matsa a gobe, idan hakan ba ta yiwuwu ba za mu matsa a jibi''.

Wakilin BBC a yankin gabas ta tsakiya Sebastian Usher yace a yanzu 'yan kasar Iran za su zuba idanbu su ga ko jawabin na shugaba Hassan Rouhni zai sauya yadda ake kallon batun na Internet ganin yadda lamarin ke shan suka musamman daga Malamai.

A shekarar 2009 da tara ne dai gwamnatin Kasar ta hana 'yancin fadar albarkacin baki ga 'yan jarida bayan boren da aka yi na kin jinin shugabannin gwamnatin Iran, saboda hana amfani da shafukan Facebook, da Twitter da kuma You Tube da suka yi.