Boko Haram:Kwankwaso ya caccaki Jonathan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jonathan na shan suka game da rikicin Boko Haram

A daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da ruruwar rikicin Boko Haram, Gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi shugaba Goodluck Jonathan, kuma babban kwamandan askarawan kasar da gazawa wajen shawo kan matsalar.

A cewarsa, ya kamata shugaba Jonathan ya tashi tsaye wajen magance matsalar dungurungum, idan dai har da gaske yake game batun.

Kwankwaso ya ce bai kamata a saka siyasa cikin lamarin ba a dunga dora wa juna alhaki tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa ba.

Gwamnan Kano din ya ce 'yan Boko Haram na kashe mutane ba tare da la'akari da addinni ko siyasa ba a don haka ya kamata a hada hannu domin magance matsalar.

Sai dai bangaren shugaban kasar ya musanta zargin da gwamnan na jihar Kano yayi kan cewar ya gaza magance rikicin.

A cewarsa dakarun tsaron kasar na iyaka kokarinsu domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

Karin bayani