'Yan gudun hijira 20,000 sun shiga Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Hukumar agajin gaggawa a Nigeria NEMA ta ce daga ranar Litinin zuwa Talata 'yan gudun hijira 20,000 ne suka shiga cikin Maiduguri babban birnin jihar Borno daga wasu garuruwa sakamakon rikicin Boko Haram.

Babban jami'in NEMA a shiyyar arewa maso gabashin Nigeria, Alh Muhammadu Kanar ne ya shaidawa BBC a hirar da aka yi da shi game da yanayin da 'yan gudun hijira ke ciki a jihar Borno.

Kanar ya ce, "Mun kirga mutane kusan 20,000 yawancinsu daga Bama, amma kuma akwai wasu daga Kawuri da Konduga wadanda duk a yanzu suke Maiduguri".

Jami'in ya kara da cewar, "Muna hada hannu da Red Cross da gwamnatin jihar Borno da kananan hukumomi don kai su sansanonin da za su zauna, mun tanadi abinci da wuraren kwana don tallafa musu."

Dubban mutane ne suka gudu daga Bama gari na baya-bayannan da 'yan Boko Haram suka kwace ranar Litinin.

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin Boko Haram ya raba mutane kusan 650,000 da gidajensu a Nigeria.

Gwamnatin Nigeria ta ce tana iyaka kokarinta domin magance rikicin Boko Haram, sai dai jama'a da dama na ganin cewar gwamnatin ta gaza wajen shawo kan matsalar.