'Boko Haram za ta iya kwace jihar Borno'

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Shekau ya ce za su kafa daular musulunci

Wani rahoton kwararru ya yi gargadin cewar watakila Nigeria ta rabe gida biyu saboda yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da karbe iko da wasu yankunan arewa maso gabashin kasar.

Rahoton da kungiyar Nigeria Security Network ta fitar, ya ce kungiyar Boko Haram a shirye take ta kwace Maiduguri babban birnin jihar Borno musamman bayan harin da ta kai a Bama.

Kungiyar ta ce "Idan har Maiduguri ta fada hannunsu, nasara ce mai muhimmanci kuma alama ce ta karfin Boko Haram tun daga soma rikicin".

Kungiyar kwarrarrun wacce ta hada da tsohon Jakadan Amurka a Nigeria, John Cambell, ta ce samun nasara a hare-haren zai baiwa Boko Haram damar kwace daukacin jihar Borno da kuma watakila wasu sassan jihar Adamawa da Yobe har zuwa kasar Kamaru.

'Rashin kwarin gwiwa'

Rahoton ya ce, "Dole ne sai an dauki matakin da ya dace, idan ba haka ba wani yanki mai fadi a Nigeria zai koma hannun Boko Haram kamar yadda kungiyar IS ta yi a kasar Iraki".

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Nigeria ta gaggauta tura karin sojoji zuwa Maiduguri domin hana garin fada wa hannun abokan gaba, sannan kuma gwamnati ta kwato wasu hanyoyi jihar Borno domin katse hanzarin 'yan Boko Haram.

Kungiyar ta yi gargadin cewar rashin kwarin gwiwa da rashin makamai na daga cikin abubuwan da ke hana sojoji murkushe Boko Haram da kuma gudu daga fagen daga.

Rahoton ya bukaci kasashen waje su kawowa Nigeria dauki musamman da kayayyakin soji.