Yunwa na barazana a Somalia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikici da kungiyar Al-Shabab na kara janyo matsala a kasar Somalia

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar mutane fiye da miliyan daya ne a Somalia ba su da wadatacciyar hanyar samun abinci.

A cewar ta matsalar za ta iya yin kamari idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

Jami'in kula da harkokin jin kai na kasar, ya ce, yanayin ya tabarbare cikin gaggawa a cikin watanni shidan da suka wuce saboda fari da tashin goron farashin abinci da kuma rikici.

Yayi gargadin cewar kananan yara dubu 200 ne ke fama da tamowa.

Karin bayani