Taswirorin Nokia a wayoyin Samsung

Hakkin mallakar hoto samsung
Image caption Kasashe 190 ne ke cikin Taswirar wayoyin Nokia

Nan bada jimawa bane taswirorin dake cikin wayoyin Nokia zasu soma bayyana a wayoyin Samsung.

Wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin kamfanonin biyu, ita zata bada damar yin hakan.

Ana yiwa wannan mataki kallon wata hanya ta taimakawa Samsung ya ware kansa daga Google wanda ke sa ido akan manhajar Android.

Ada da aka fi sani da taswirorin Nokia, kamfanonin Yahoo da Amazon da Garmin na amfani da taswirorin.

Kasashe 190 ne ke cikin wannan Taswira ta Nokia.

Tana kuma samar da bayanai ga masu yawan bude ido da kuma bayanan sufuri

Buku da kari za'a iya sauke taswirorin ga wata na'ura domin a iya amfani da su ba lallai sai da Intanet ba.

Da yake rubutu a Ars Technica , Ron Amadeo ya ce taswirorin nokia na daya daga cikin abubuwan da Samsung yake son ganin ya samu domin ya rage dogaro da Google.