Kotu a Amurka Tuhumi Kamfanin mai na BP

Kamfanin mai na BP Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kamfanin mai na BP

Wata Kotu a Amurka ta kama kamfanin mai na BP da laifin sakaci dangane da malalar mai a gabar Tekun Mexico, a shekara ta 2010.

Sakacin da kotun ta ce ya haddasa bala'in malalar mai da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Amurka.

Darajar hannun-jarin kamfanin ta yi matukar faduwa bayan wannan hukunci da kotun ta yi.

Hukuncin ya janyo wa Kamfanin man na BP tara ta biliyoyin daloli, baya ga kudaden da kamfanin ya biya a matakan sasantawa da wasu bangarori daban-daban.

Wata sanarwar da Kamfanin ya fitar ta ce Kamfanin bai amince da wannan hukuncin ba, kuma zai daukaka kara.

Kimanin ma'aikata goma sha daya ne suka mutu, lokacin da wani matonin mai na Deepwater Horizon ya balle, ya kuma nutse a gabar Tekun Mexico.