APC:Buhari da Kwankwanso za su yi takara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An jima ana tababa a kan ko Janar Buhari zai tsaya takara

Wasu magoya bayan tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari sun ce, tabbas zai fito neman takarar shugabancin kasa a zaben da za' a yi a badi.

A fagen siyasar Najeriyar dai ana ta tababa a kan ko Janar Buharin zai sake fitowa takara a jam'iyyarsu ta APC mai adawa.

Hon Faruk Adamu Aliyu, makusanci Janar Buharin shine ya tabbatarwa da BBC shigar Buharin takara a zabe mai zuwa.

'Takarar Muhammadu Buhari tana nan daram dam' in ji Hon. Faruku Adamu Aliyu.

Kwankwaso ma yana tuntuba akan tsayawa takarar

Wani na hannun daman Janar Muhammadu Buharin kuma gwamnan jahar Kano Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso shima ya ce yana kan tuntubar magoya baya domin yanke shawarar tsayarwarsa takara.

Gwamnan ya ce kodayake bai kaiga ayyana takarar tasa ba, amma mutane da dama a ciki da wajen jam'iyyar su ta APCn na yi masa kiraye- kirayen ya fito.

Masana harkokin siyasa na kallon za a iya samun baraka a jam'iyyar adawa ta APC mai neman karbe iko daga PDP idan aka zo maganar wanda jam'iyyar zata baiwa tutar takarar Shugaban Kasa.

To sai dai Gwamnan Kano ya ce babu wani sabani tsakaninsa da Janar Muhammadu Buhari akan maganar takarar.