Ebola: Za a rage hutun makarantu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kara hutun makarantu ne saboda cutar Ebola a Nigeria

Gwamnatin Nigeria ta sanar da cewa za a bude makarantu a fadin kasar a cikin watan Satumbar da muke ciki a maimakon watan Oktoba.

A watan Agusta ne hukumomi a kasar suka sanar da kara wa'adin hutun da makarantu ke yi zuwa watan Oktoba mai kamawa saboda a samu damar shawo kan bazuwar cutar Ebola da ta barke a kasar.

Cutar Ebola ta hallaka mutane bakwai a Nigeria tun lokacin da dan kasar Liberia, Patrick Sawyer ya shigo da cutar cikin kasar.

Hukumar lafiya ta duniya dai ta kiyasta cewa mutane dubu daya da dari tara ne suka rasa rayukansu a Yammacin Afrika tun bayan barkewar cutar a watan Fabarairun wannan shekarar.