Takunkumin sayen makamai kan Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta Kudu

Wasu Kungiyoyin kawance na agaji sun yi kira ga kasashen duniya da a sanya wa kasar Sudan ta kudu takunkumin hana sayen makamai.

Rikici tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a kasar ya tilasta wa mutane sama da miliyon daya da dubu dari biyar barin gidajensu.

Kawancen Kungiyoyin mai mambobi sama da talatin, ya ce dukkan bangarori biyun na samun makaman da suke fada da su ne ta hanyar sayowa daga kasashen wajen.

Ya kuma bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa ciki har da Majalisar Sulhu ta Majalisar Dinkin Duniya da su haramta safarar makamai zuwa kasar Sudan ta kudu.