Shirin tsagaita wuta na Ukraine da Rasha

Shugabanin Rasha da Ukraine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dai dade ana gwabza fada tsakanin dakaraun gwamnatin Ukraine da 'yan a ware magoya bayan Rasha a gabashin kasar.

Nan gaba kadan ne shugabannin kasashen duniya za su gana da shugaban Ukraine Petro Proshenko gabannin taron kungiyar tsaro ta NATO da za a gudanar a Wales.

Mr Proshenko zai yi wa Amurka da shugabannin tarayyar bayanin yadda tattaunawarsu ta kasance da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

Ana sa ran taron na kwanaki biyu, zai maida hanakali akan rikicin na Ukraine, sai dai shugabanni za su tattauna akan karuwar masu tada kayar baya na mayakan Islama a iraqi da kuma syria.

Masu aiko da rahotanni dai sun ce jawabin da Mr Proshenko zai yiwa shugaba Obama na Amurka, da prime ministan burtaniya David Cameron da shugabannin faransa da italiya da kuma Jamus alamu ne na nuna cikakken goyon baya ga shugaban na Ukraine.

A jiya laraba ne Mr Proshenko ya ce ya amince da shirin tsagaita wuta, bayan tattaunawa da shugaba Putin ta wayar tarho, wanda yace ya na fatan za su cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tattaunawar da za su yi da shugabannin 'yan adawa a gobe juma'a.

Sai dai a wata tattaunawa da BBC sakatare janal na kungiyar NATO Anders Fgogh Rasmussen yace shirin tsagaita wuta da shugaban Rasha ya fito da shi babu gaskiya a cikinsa.

Ita ma Faransa ta janye aike wasu shiragen yaki biyu da za a kai Moscow saboda kutsen da Rasha ta yi a rikicin Ukraine.