'Mutane 800,000 na kashe kansu a duk shekara'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan wasan kwaikwayo, Robin Williams na daga cikin wadanda suka kashe kansu a bana

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa sama da mutum dubu dari takwas ne ke kashe kansu a kowace shekara.

Hukumar ta bayyana cewa dabi'ar kashe-kai wata babbar matsala ce da ta zama wajibi a shawo kanta, tana gargadin cewa yadda kafafen yada labarai ke ba da labarin kashe kai na daga cikin hanyoyin da wasu kan bi su halakan kansu ta hanyar da suka wasu suka bi a baya.

A cewar hukumar, adadin maza ya fi yawa a tsakanin masu kashe kansu idan aka kwatanta da mata, wadanda galibi suka kai shekara saba'in da haihuwa.

Jonny Benjamin, wani mai rajin kare lafiyar mutanen da suka samu tabuwar kwakwalwa ne, wanda kuma ya taba yunkurin halaka kansa a baya yace akwai bukatar a wayar da kan jama'a wajen agaza wa mutanen da rayuwarsu ke fuskantar hadari.