An kashe shugaban Al-Shabab a Somalia

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Mayakan Al-Shabab a Somalia

Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta ce dakarun kasar sun kashe shugaban kungiyar Al-Shabab, Ahmed Abdi Godane.

Amurka ta ce ta kashe Godane ne sakamakon luguden wuta ta sama da ta kaddamar a Somalia a karshen makon da ya wuce.

A cewar Amurka kashe shugaban Al-Shabab babbar nasara ce ga yaki da ta'addanci da take yi.

Al-shabab ta kaddamar da hare-hare da dama a Somalia da kuma wasu kasashen Afrika inda ta hallaka mutane da dama.

Kungiyar Al-Shabab a shekara ta 2012 ta yi wa kungiyar Alka'ida mubaya'a.

Ahmed Godane ya karbi ragamar jagorancin kungiyar ne a shekara ta 2008, kuma a shekarar ta 2012 ne Amurka ta sanar da tukwicin dala miliyon bakwai a kansa.

Karin bayani