Mutane na ficewa daga Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane na tserewa daga manyan garuruwan jihar Borno

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na nuna cewar mutane da dama suna ficewa daga garin saboda tsaron rikicin Boko Haram.

Bayanai sun nuna cewar iyalai da dama suna ta tserewa daga birnin zuwa makwabtan jihohi domin neman mafaka saboda rashin tabbas din da suka shiga a Maiduguri da sauran biranen jihar ta Borno.

Tun bayan da kungiyar Boko Haram ta karbe iko da wasu manyan garuruwan jihar Borno mutane suka soma fargabar cewa watakila birnin Maiduguri ya kasance gari na gaba da Boko Haram za ta kaddamar da hari a cikinsa.

Tun daga watan Agusta kungiyar Boko Haram ta soma kwace garuruwan jihar Borno bisa abinda kungiyar ta kira kafa daular musulunci.

Bayanai sun nuna cewar a yanzu haka garuruwan Dikwa, da Marte, da Gwoza, da Gamborou Ngala da Damboa , da kuma Buni Yadi(jihar Yobe), duk sun koma karkashin ikon Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya tilasta wa dubban mutane barin muhallansu.