An rage hutun makarantu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban makarantun Framare a Nigeria

Mahukunta a Nigeria sun rage tsawon hutun da suka kara wa daliban wasu makarantun kasar, wanda aka kara tun da farko, sakamakon bullar cutar Ebola a kasar.

Ministan ilimin kasar, Mallam Ibrahim Shekarau, ya ce a yanzu za a bude makarantun ne a ranar 22 ga watan Satumba, sabanin 13 ga watan Oktoba da hukumomin suka bayyana tun da farko.

Ministan ya ce sun sauya shawarar ne bayan hukumomin lafiya a kasar sun tabbatar musu cewa Nigeria ta na gab da kawar da cutar Ebola, saboda haka babu wata fargaba.

Cutar ebola a yammacin Afirka tayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 2,000 sannan kuma 400 daga cikinsu sun rasa rayukansu ne a makon daya gabata kadai.