Ana ci gaba da gwabza fada a Ukraine

Sojojin da ke marawa Rasha baya. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun sojin Ukraine dai na ci gaba da bata kashi tsakanin su da 'yan a aware magoya bayan Rasha a gabashin kasar.

Ana cigaba da gwabza mummunan fada a Ukraine wurare garin Mariupol na gabar teku dake kudu maso gabashin Kasar.

Wanda shine kuma Gari na karshe dake hannun dakarun gwamnati, wanda jama'ar garin suka kai rabin miliyan.

Tunda farko an ji karar harbin makaman atilare a Donesk a birnin, inda ko a makon da ya wuce 'yan tawaye sun yi barazanar kaddamar da hare-hare a cikin birnin.

Wani wakilin BBC yace akwai mutane da dama da suka gigita saboda fada.