Mutane sun tsere daga Gulak da Michika

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Najeriya

Rahotanni daga Nijeriya na cewa daruruwan mutane ne ke neman mafaka a wurare daban daban, bayan da suka tsere daga garuruwan Gulak da Michika a jihar Adamawa yayin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kori sojojin kasar.

Bayanai na nuna cewar hakan ya faru ne bayan da sojojin suka yi yunkurin karbe ikon garin Madagali dake hanun 'yan kungiyar ta Boko, lamarin da ya cutura ya kuma sa sojojin suka tsere.

Rahotani sun kuma ce lamarin ya sa daruruwan mutane tserewa daga garuruwan domin neman mafaka a akan tsaunuka

A jiya Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce hare-haren kungiyar Boko Haram, suna barazana ga 'yanci da hadin kan kasar, amma ta ce ta dukufa wajen ganin ta yi galaba akan 'yan ta'adda, da kuma kare martaba da iyakokin kasar.

Hedkwatar tsaron ta ce ba martabar rundunar sojin kasar ce kadai ke neman zubewa ba, sakamakon ayyukan kungiyar ta Boko Haram, har ma da kimar Najeriyar baki daya.