Kotu ta amince da cire kariyar Hama

Niger Hakkin mallakar hoto
Image caption Rahotanni baya bayan nan sun ce Hama ya tsallaka zuwa kasar Belgium

A Jamhuriyar Nijar, kotun tsarin mulkin kasar ta jaddada sahihancin matakin cire wa shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu rigarsa ta kariya da kwamitin gudanarwa na majalisar ya dauka kwanakin baya.

Kotun ta ce matakin ya zo daidai da doka mai lamba 88 ta kundin tsarin mulki wadda ta ce kwamitin majalisar na iya daukar matakin cire wa dan majalisa kariya, koda majalisar ba ta cikin zama.

Ya zuwa yanzu dai, magoya bayan shugaban majalisar ba su ce uffan ba, suna masu cewa sai sun yi nazarin hukuncin kotun tukuna.

A kwanakin baya ne shugaban majalisar malam Hama Amadu ya shigar da kara a gaban kotun tsarin mulkin, yana kalubalantar matakin kwamitin majalisar cewa ba a dauke shi a bisa ka'ida ba.