Boko Haram: SSS za ta binciki Sheriff

General Ihejireka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption General Ihejireka

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya SSS ta wanke tsohon hafsan hafsoshin kasar Laftanal Janar Azubuike Ihejirika daga zargin da ake yi masa na tallafawa kungiyar Boko Haram.

Sai dai kuma hukumar ta ce zata gayyaci wanda ake zargin na su tare wato tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff don amsa wasu tambayoyi kan zargin.

Wani dan kasar Australia mai shiga tsakanin Kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin Najeriya kan sakin 'yan matan Chibok da kungiyar ta sace Dr. Stephen Davis ya bayyanawa wasu kafafen yada labarai cewar, mutanen biyu na taimakawa kungiyar.

Zargin kuma da suka musanta.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba