Twitter ya samu sabani da Twitpic

Twitter Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Twitter ya ce ya kalubalanci Twitpic ne domin kare tambarinsa

Kamfanin nan dake samar da hotuna na Twitpic a dandalin Twitter, zai daina gudanar da ayyukansa saboda wata takaddama da ta kaure tsakaninsa da kamfanin Twitter.

Takaddamar ta samu ne saboda sabanin ra'ayin da suka samu kan batun tambari gudanar da kasuwanci.

Kamfanin na Twitpic, wanda aka bude shi a 2008, ya ce kamfanin Twitter ne ya nemi ya rufe wata manhajarsa ko kuma a hana shi kafar samun shiga dandalin na Twitter.

Kamfanin na Twitter ya ce bai ji dadi ba da lamarin ya kai ga za a rufe kamfanin na Twitpic, kuma da zai so ya ci gaba da mafani da sunansa.

Shi dai kamfanin na Twitpic ya kasance shi yake baiwa masu amfani da shafin Twitter damar aikawa da raba hotuna.

"Muna masu bakin cikin ganin cewa za a rufe Twitpic." wata sanarwa da kamfanin Twitter ya fitar a rubuce ta bayyana.

Kamfanin na Twitter ya kara da cewa, sai dai ya zama dole su ci gaba da kare muradan kamfaninsu ciki har da tambarin kamfanin.

Tuni dai Twitter ya bayyan cewa ya samar da wani zabi da zai dinga baiwa masu amfani da shafin nasa damar aikawa da kuma raba hotuna kamar yadda kamfanin Twitpic ke yi a baya.