Boko Haram sun karbe iko a Minchika

Yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan gudun hijira a Najeriya

Rahotani daga jihar Adamawa sun ce 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun karbe iko a garuruwan Minchika da Bama.

Sun ce karar harben harben bindigogi da aka rika ji sun lafa sai dai kawo yanzu ba bu sojoji a yankin.

Haka kuma kawo yanzu mahukunta basu ce komai ba akan halin da ake ciki a garin Minchika.

Sai dai wasu mutane sun shaidawa BBC cewa sun ga sojoji na danawa zuwa Minchika .

Bayanai sun ce Minchika babban gari ne a arewacin jihar Adamawa