Matsalar satar wayoyin tafi da gidanka a Birtaniya

Wasu alkaluman kididiga sun nuna cewa me yuwuwa wayoyin tafi da gidanka da kamfanin Apple ya fitar a baya bayanan na cikin wayoyin da aka fi sace wa a Birtaniya da kuma yankin Wales daga shekarar 2012 zuwa watan janairu na shekarar 2014.

Wani bincike da ma'aikatar cikin gida ta Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa wayoyin tafi da gidanka irinsu Iphone5 da 5c da 5s da kuma 4s da kuma blackberry 9790 na cikin wayoyoyin da aka fi sacewa .

Hakkin mallakar hoto Getty

Haka kuma wayoyin Samsung da HTC na cikin wadanda lamarin ya shafa

An dai gano haka ne a nazarin da aka yi akan miyagun laifuka a Landan

Kamfanin Apple ya ce yana kokarin samar da kariya akan wayoyin da mutane ke amfani da su.

Binciken ya ce sabbin matakan tsaro da dauka zasu taimaka wajen rage yawan sace sacen wayoyin tafi da gidanka.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Binciken ya kuma ce mata da matasha masu shekaru 14 zuwa 24 na cikin rukunin da aka fi sacewa waya.

Sakatariyar ma'aikatar cikin gida ta Birtaniya Theresa May ta ce duk da cewa an samu raguwa a yawan masu aikata miyagun laifuka karkashin gwamnatin hadin gwiwa sai dai kawo yanzu matsalar yawan sace sacen wayoyoyin na cigaba da janyo damuwa .

Ta ce mutane na tafiya tare da bayanai masu muhimanci kamar bayanan kudi da sakonin email da kuma sauran bayanai da ake samu ta wayayoyin salula.

Ta ce shi yasa hakan yake da muhimanci ga gwamnati da 'yansanda da kuma kamfanonin wayoyin su hada karfi da karfe wajen tunkarar matsalar.