Boko Haram ta kwace garin Minchika

Harin 'yan kungiyar Boko Haram a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Harin 'yan kungiyar Boko Haram a Najeriya

Rahotanni daga jahar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki cikin garin Minchika.

Mazauna garin da dama da suka hada da mata da yara da tsofaffi ne suka gudu daga garin.

Bayanai na nuna cewa an tura jami'an sojoji domin samar da tsaro, inda ake iya gani wani jirgin sama na shawagi a cikin garin.

A kwanaki biyun da suka gabata ma 'yan kungiyar Boko Haram din sun kai hari garin Gulak dake makwabtaka da garin na Minchika duka a jihar ta Adamawa suka kuma fatattaki mutanen garin.

'Yan kungiyar na cigaba da dannawa wasu garuruwan jihar ta Adamawa mai makwabtaka da jihar Borno ta yankin kudanci.

Tuni dai kungiyar ta kwace ikon garuruwan Gwoza, da Bama, da Banki,da Gamborun Ngala, da Dikwa a jihar Borno.