Tangarda a gwamnatin hadin kan Falasdinu

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto r
Image caption Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi barazanar ballewa daga shirin gwamnatin hadaka da Hamas idan ta ki amincewa da cikakken hadin gwiwa a Gaza.

Abbas yace idan Hamas ta ki amincewa da gwamnati daya tilo ta Falasdinawa da kundin tsarin mulki daya to kuwa wannan kawance ba zai yiwuwa ba.

Ya kara da cewa wajibi ne gwamnatin tsakiya ta kasar Falasdinu ta kasance mai iko da dukkan bangarori ta kuma yanke hukunci akan shiga yaki da kuma wanzar da zaman lafiya.

An dai dauki shekaru mai tsawo kafin a cimma sasantawa tsakanin bangarorin Falasdinawan guda biyu.

Bukatar hadin kan da kuma sasantawar ta biyo bayan karin matsin lamba ne a lokacin luguden wuta ta baya bayan nan da Israila ta yi a Gaza.

Karin bayani