Yarjejeniyar Ukraine ta fara samun cikas

Ukraine Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan sabon rikici zai iya barazana ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma

A kasar Ukraine, rahotanni sun ce an ji wasu fashe fashe a garin Mariupol dake gabashin kasar.

Hakan ya sa kasashen duniya da ke kokarin ganin an sasanta rikicin suka fara nuna shakkunsu kan dorewar yarjejeniyar da aka cimma ranar juma'a da ta gabata.

Bayanai na nuna cewa, wasu 'yan aware ne suka lalata wani shingen bincike mai muhimmanci ga gwamnati ta hanyar yin amfani da makamai na atilari.

Rahotannin sun kuma nuna cewa sojojin Ukraine suma sun mayar da martani kan 'yan awaren.

Masu boren na yiwa garin Mariupol kallon gari mai matukar muhimmanci ganin cewa ya na kusa da garin Crimea da suka fi rinjaye.