'Sojojin AU na yi wa mata fyade a Somalia'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar AU ta ce za ta binciki zargin

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi wasu sojojin da ke rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka da ke kasar Somaliya da yin fyade ga wasu mata da kananan yara.

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil'aman ta fitar, ya ambato wasu mata su ashirin da daya da suka ce wasu sojojin kasar Burundi da Uganda sun yi amfani da larurarsu ta rashin wasu muhimman abubuwan bukatun rayuwa wajen yin lalata da su da sunan za su taimaka musu.

Kungiyar ta ce an ci zarafin matan ne a lokutan da suke neman agaji ta fuskar magani ko ruwan sha a sansanonin Kungiyar tarayyar Afirka.

Sai dai kungiyar Tarayyar Afirkan - AU ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin.