Labaran BBC Hausa a talabijin

BBC
Image caption Labaran BBC Hausa a talbijin shi ne na farko a duk fadin duniya

Yau ne sashen Hausa na BBC zai fara gabatar da labaransa ta kafar talbijin, a wani abu da shi ne irinsa na farko ga tashoshin watsa labarai na duniya.

Shirin labaran BBC Hausa a Talbijin na minti 10, zai rika kawo labaran Afirka da ma na kasashen duniya ga masu kallo ta tashar Capital TV da ke Kaduna a Nijeria da kuma tashar tauraron dan adam da ke Afirka ta yamma ta Adom TV.

Za a rika gabatar da shirin ne a ranakun mako wato Litinin zuwa Juma'a, zai kuma dinga gudana kai tsaye a shafin intanet na bbchausa.com.

" A cikin wannan shiri sabo na talbijin, muna fatan kawo wa jama'a masu kallo da masu saurare irin rahotanni da ke faruwa a duniya, wadanda kuma muke tsammanin za su ba su sha'awa kuma za su shafi harkokin rayuwarsu." In ji Editan BBC Hausa, Mansur Liman.

Image caption Aichatou Moussa da Elhadji Diori Coulibaly su ne za su dunga gabatar da shirin

Sabon shirin labaran Talbijin na sashen Hausa na BBC, kari ne a kan shirye-shiryensa na rediyo, da intanet da kuma ta hanyar wayoyin salula.

"Wannan kuma wani bangare ne na irin matakan da BBC ke dauka da muka tabbatar da cewa ta dace da zamani." Liman ya kara da cewa.

Za dai a iya ganin shirin kai tsaye ta gidan Talbijin na adom TV da ke tauraron dan adam da kuma shafinmu na intanet wato bbchausa.com da misalin karfe tara na dare a agogon Nijeriya da Nijar.

Sannan gidan talbijin na Capital TV da ke Kadunan Najeriya shi ma zai nuna shirin Labaran Talbijin na BBC da misalin karfe goma na dare agogon Najeriyar.