'Boko Haram ta kwace garuruwa 10'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane sun tsere daga gidajensu

Rahotanni daga arewacin Nigeria na cewa yanzu haka garuruwa sama da goma ne ke karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram.

'Yan kungiyar sun kwace wadannan garuruwa ne a cikin jihohi uku na arewacin kasar inda aka saka dokar ta baci, watau Borno da Yobe da Adamawa.

A ranar Lahadi ne Boko Haram ta kwace iko da garin Michika a jihar Adamawa, kwanaki biyu bayan kwace garin Gulak.

Wasu mazauna garin Michika da kuma Gulak da suka tsere, sun bayyana cewa ana zaman zulumi a garuruwan, kasancewar mayakan kungiyar sun yi ta harbe-harbe, kuma an yi hasarar rayukan jama'a.

Sun ce maharan sun ci gaba da fakewa a cikin gidajen jama'a, lokacin da jirgin yakin sojojin Nigeria. ke shawagi a saman garin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa jami'an tsaron na shirin kai farmakin sake kwato garin Bama , a yayin da garin Mubi na jahar Adamawa ke fuskantar barazana.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service