Boko Haram: An harbi ɗan Obasanjo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cif Olusegun Obasanjo ya ce Boko Haram ta gagari gwamnatin Jonathan

Rahotanni daga Nigeria na nuna cewar, an harbi ɗan tsohon shugaban kasar, Janar Olusegun Obasanjo a wata fafatawa da aka yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan Boko Haram.

Wani na hannun damar Cif Obasanjo ya tabbatar wa da BBC cewar an harbi Laftanar Kanal Adeboye Obasanjo amma kuma baya cikin mummunan yanayi.

Malam Mohammad Keffi ya bayyana cewar " An harbe Adeboye ne a lokacin da suka baro Mubi suna kan hanyar Michika sai 'yan Boko Haram suka kai musu hari a cikin ayarin dakarun Nigeria".

Bayanai sun nuna cewar an yi gumurzu tsakanin 'yan Boko Haram da dakarun Nigeria a garin Bazza da ke kusa da garin Mubi na jihar Adamawa inda 'yan Boko Haram suka harbi wasu sojoji ciki har da Adeboye Obasanjo.

Rahotannin sun ce Adebayo Obasanjo yana da mukamin Laftanar Kanal a dakarun sojin Nigeria kuma injiniya ne da ke bataliya ta uku da ke Jos a jihar Filato.

Rikicin Boko Haram ya hallaka dubban mutane a Nigeria ciki hadda dakarun kasar.