Matar Yarima William ta kara samun ciki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yarima William da Kate

Duchess ta Cambridge watau matar Yarima William na dauke da juna biyu, na haihuwar danta na biyu kenan.

Fadar Kensington ta ce kamar yadda Duchess din ta yi fama da laulayi lokacin tana dauke da cikin Yarima George, a yanzu haka ma tana fama da zazzabin safe kuma likitoci na lura da ita a cikin fadar.

Sanarwar ta ce Sauraniya Elizabeth da iyalan gidan sarautar Birtaniya duk suna farin ciki a kan da labarin.

Abin da Yarima William da Kate za su haifa na biyu zai kasance na hudu a jiran gadon sarautar Birtaniya.

Firaministan Birtaniya, David Cameron da shugaban jam'iyyar Labour Ed Miliband da kuma Archibishop na Canterbury duk sun aike da sakonsu na taya Yarima William da Kate murnar wannan ciki da ta samu.