Serena ta lashe US Open

 Serena Williams Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shine karo na shida Serena na lashe gasar US Open

'Yar wasan Tennis ta daya a duniya, Serena Williams ta lashe kofin gasar US Open a karo na shida a bangaren mata.

Williams 'yar kasar Amurka ta samu nasarar ne bayan da ta doke Caroline Wozniacki 'yar kasar Denmark da ci 6-3 6-3.

'Yan wasan sun kwashe minti 75 suna fafatawa.

Yanzu Williams tana da kofunan manyan gasar tennis 18 yayin da wannan kofin na US Open shine karo na uku a jere da ta lashe shi bayan ga wasu nasarori uku da take da su a baya.

Hakan na nufin 'yar wasan, mai shekara 32 ta lashe gasar sau shida ke nan.