'Kamaru ta kashe 'yan Boko Haram 100'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na jira kota kwana a kan iyakokin kasarta

Gwamnatin Kamaru ta ce sojojinta sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 a lokacin da mayakan kungiyar ke kokarin kutsawa cikin kasar.

Sanarwar da gwamnatin Kamaru ta fitar ta ce 'yan Boko Haram sun harba makaman roka biyu daga garin Fotokol da ke lardin arewa mai nisa, abinda ya sa dakarun Kamaru suka maida martani har mayakan Boko Haram fiye da 100 suka mutu.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin na dakarun Kamaru.

Gwamnatin Kamaru bisa matakan tsaro ta sanar da rufe wasu makarantu da ke lardin arewa mai nisa.

Tuni 'yan Boko Haram suka kwace garin Gamborou Ngala da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.

Karin bayani