Google zai shirya taron jin bahasin jama'a

Hakkin mallakar hoto Reuters

Google zai shirya tarukan jin bahasin jama'a a sassan turai daban daban domin tafka mahawara akan hukuncin da wata kotu a turai ta yanke game da yancin cire wasu bayanai a shafukan internet.

Wata kotu a Turai ta baiwa mutane damar neman Google ya cire wasu bayanai game da su a shafinsa na internet.

Sai dai Google na adawa da hukuncin, da ya sa mutane fiye da dubu casain shigar da bukatar cire bayanai gamedasu da ya wallafa a shafinsa

Wani kwarare ya nuna shakku akan tarukan jin bahasin jama'a, a cewarsa taruruka ne da zasu fi maida hankali wajen inganta martabar kamfanin a maimakon tattaunawar da za'a yi.

A ranar 9 na watan da mu ke ciki za'a soma gudanar da tarukan a birnin Madrid yayinda za'a gudanar da sauran taruka shida a wasu birane turai kafin ranar 4 ga watan Nuwamba.

Wani kwamiti da kamfanin Google ya kafa bayan hukuncin kotun shi ne zai jagorancin tattaunawar.

Kwamitin ya kunshin mutane irinsu Jimmy Wales wanda shi ne ya kirkiro Wikimedia da kuma tsoffin alkalai .

Google na neman gudumuwar kwararu da zasu yi magana a tarukan da ya ce an shirya su ne domin a tattauna akan batun yancin cire bayanan mutane daga shafinsa da kuma yancin samar da bayanai ga alumma.

Hakkin mallakar hoto getty

Sai dai hukuncin ya shafi kasashen dake Turai ne kawai.

Google ya ce umarnin cire wasu bayanai sabon tsari ne kuma abu ne mai wuya kuma yana bukatar taimako game da matakin da zai dauka wajen cire wasu bayanai ko akasin haka.

Tun a tsakiyar watan yulin daya gabata ne Google ya rika samun koke koken mutane dubu casain da suka nemi a cire bayanai da ya shafi rayuwarsu.

Bukatar ta hada da cire bayanai akan shariar da aka yi wa wasu da ake zarginsu da aikata miyagun laifuka da kuma wasu hotuna da suka nuna ana cin zarafin mutane .

An dai yi ammanar cewa kamfanin ya amince da rabin bukatun masu korafi sai dai mutane zasu iya daukaka kara idan ba'a amince da bukatunsu ba.