Marin Cilic ya lashe US Open

Marin Cilic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marin Cilic shine dan Croatia na farko da ya lashe gasar US Open

A karon farko Marin Cilic dan kasar Croatia ya lashe gasar US Open a bangaren maza bayan da ya doke Kei Nishikori dan kasar Japan da ci 6-3 6-3 6-3.

Wannan nasara ta bashi damar kasancewa dan kasar Croatia na farko da ya taba lashe daya daga cikin manyan gasar wasan tennis a duniya tun bayan mai horas da shi, Goran Ivenisevic da ya taba lashe gasar Wimbledon a 2001.

"Ban san yadda na yi na samu nasara ba, ina ganin hazakar da nuna cikin 'yan shekarun nan ne musamman ma a wannan shekara ta karshe." In ji Cilic.

Dan shekaru 25, Cilic, wanda ke matsayi na 14 a jerin wadanda suka kware a buga wasan tennis a duniya, ya doke Tomas Berdych da Roger Federer a baya kamin ya kai ga lashe kofin.