Soji na yunkurin kwace garuruwan Adamawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta kwace garuruwa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa

Rundunar Sojin Najeriya ta ce tana kai hari kan mayakan Boko Haram a yunkurin kwato garuruwan da kungiyar ta kwace a jihar Adamawa.

Rundunar ta ce ta kashe mayakan Boko Haram da dama tare da raunata wasu, sai dai ita ma jami'anta biyar sun samu raunuka.

Dakarun dai na yunkurin sake kwace garuruwan Michika da Gulak da Bazza da kuma Madagali da kungiyar Boko Haram ta kwace a jihar a karshen mako.

Jama'a na cikin zullumi, yayin da wasu dubbai ke tsere wa garuruwan da ake gabza fadan.

Karin bayani