Karancin abinci a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sudan ta Kudu ce kasar da aka kafa mai karancin shekaru a duniya

Wakilin BBC Emmanuel Igunza ya ziyarci wani kauye a Sudan ta Kudu, inda mutane suka dogara da cin bado yayin da ake fargabar fari a kasar.

Sanyin safiya ne a kauyen Reke, wanda ke da mazauna kimanin 3,000 wadanda suka tsere wa fada tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a jihar da ke da arzikin mai ta Unity.

An sheka ruwan sama a cikin dare a kauyen da ke da nisan kilomita 650 daga Juba, kuma sai motoci masu karfin inji ne ke iya zuwa kauyen.

Yara suna wasa a wani fili, a wani lungu kuma ga mata suna gina bukka, wanda ake kira Tukul.

Yunwa

Mafi yawa daga mazauna kauyen dai 'yan kabilar Nuer wadda shugaban 'yan tawaye Riek Machar ya fito ne.

Shugaba Salva Kiir wanda ya fito daga kabilar Dinka ya zargi Machar da kitsa yunkurin yi masa juyin mulki a watan Disamba.

Reik ya musanta zargin, amma kuma ya jagoranci 'yan tawaye su yaki Shugaba Salva.

Fiye da mutane 1.5 miliyan ne suka rasa matsugunansu sakamakon yakin da ake yi a tsakanin kabilun.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Sudan ta Kudu na gab da fadawa cikin yunwa.

Mutane a kauyen Reke sun dogara ne da agajin abinci daga hukumar abinci ta Majalisar, abinci da ba kasafai ake samu ba.

Saboda haka mutanen Reke sun dogara ne kan badon da suke debowa a wani rafin da bashi da nisa, su kan debo irin badon su nika, su kwaba da ruwa sannan su dafa su ci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan hudu na fuskantar yunwa, bayan lokacin shuka ya wuce manoma basu samu zuwa gona ba.

Masana sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar Sudan ta Kudu ta fada cikin fari mai tsanani nan da karshen shekara.