Apple ya kaddamar da agogo komai da ruwanka

Image caption Agogon baya aiki sai da iphone

A ranar Talata ne shugaban kamfanin Apple, Tim Cook wanda ya gaji Steve Jobs ya kaddamar da agogo-komai da ruwanka a gaban jama'a a jihar California.

Kamfanin na fatan duk wani mai matsakaicin hali zai iya mallakar agogon.

Sai dai tambayar a nan ita ce agogon yana da abubuwan da za su sa kasuwar abin hannu na fasaha ta farfado?

Wani mai sharhi a cibiyar bincike ta Forrester, James McQuivey, wanda kuma ya ga kaddamar da wayar iphone da kwamfutar tafi-da-gidanka ta ipad na tunanin hakan.

"Mutane sun san suna bukatar agogo kuma suna bukatar wayar komai-da-ruwanka. Kuma Apple ya hada wadannan abubuwa waje daya a abin da ya fi kowane dayansu."

Image caption Wasu za ba za su ji dadin aika sakonni ko karanta su ba a gaogon fiye da a wayar iphone

Amma ya bayyana cewa babu wata " gawurtacciyar manhaja " a agogon.

Inda ya bayar da misali cewa samar da agogon ba wai yana nufin sanya mutumin da ba ya iya amfaniu da kayan fasaha na zamani a rana daya ya fara amfani da agogon ba.

A waje daya kuma Apple ba ya tallata agogon nasa ga masu tsoron sauyin da fasaha ke janyowa ko kuma wadanda ma ba su da masaniya game da irin wadannan kayan fasaha.

Sai dai Angela McIntyre ta cibiyar bincike ta Gartner ta yi nuni da cewa ko da ya ke agogo na da takaitaccen abin da zai iya yi, Apple na yunkurin wani kamfani ya yi masa manhajoji, abin da zai sa ya fito da wasu sabbin abubuwa a lokacin da za a fara sayar da shi a badi.