'Ba na son yankin Scotland ya balle'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Cameron da Clegg da kuma Miliband duk sun isa Scotland

Firayi ministan Birtaniya, David Cameron na tattaunawa da al'ummar yankin Scotland, musamman ma wadanda za su kada kuri'ar-raba-gardama a kan makomar yankin da za yi a makon gobe.

Matakin Mr Cameron na da nufin jan-ra'ayin motanen ne da kada su goyi bayan ballewar yankin daga Birtaniya.

Mr Cemeron ya ce zai yi matukar bakin-ciki idan suka goyi bayan ballewa.

Firayi ministan na wannan kiran ne a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa ra'ayin masu goyon bayan ballewar na nema ya rinjaye na masu adawa da hakan.

Cameron ya isa Scotland din ne rana daya da shugaban jam'iyyar Labour, Ed Miliband da kuma mataimakin Firayi minista Nick Clegg.