Facebook ya nemi afuwa akan talla.

Tambarin shafin sada zumunta na Facebook Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook dai ya nemi afuwar iayyen Jariri Hudson bisa cire hoton da ya yi.

Shafin sada zumunta da muhawara wato Facebook ya nemi ahuwar iyayen wani Jariri akan haan su yin tallan hoton jaririn dan neman taimako.

Iyayen Jaririn mai suna Hudson Bond su na zaune ne a arewacin birnin Carolina na kasar Amurka, kuma su na ta kokarin samun kudaden tallafi da za su iya biyan likitoci domin su yi wa yaron dashen zuciya.

Kamar sauran kungiyoyin da ke butar taimako, mahaifin Hudson ya yi amfani da shafin na sada zumunta domin neman taimako.

Sai dai mahaifin Jaririn mai suna Mr Kevin Bond yace Facebook ya dakatar da hoton da ya wallafa na jaririn na sa, inda ya kira hoton da cewar abin firgici ne.

Mr Bond dai ya yi amfani da hoton jariri Hudson da ke makale da wasu na'urori a hancinsa, da bakinsa da kuma goshinsa, ka na kuma fuskarsa ta sauya launi zuwa jazur.

Sai dai a nasa bangaren Facebook ya wallafa wata sanarwa da ke cewa ya na neman afuwar Mr Bond na cire wannan hoto.

Inda kakakin Facebook ya kara da cewa '' A gaskiya wannan kuskure ne daga bangaren mu, kuma mun sake bada damar sake bude shafin. Dan haka mu na bada hakuri akan duk wani bacin rai da muka janyowa iyayen wanan jariri''.

Mr Bond yace ya ga sanarwar da Facebook ya fitar na ban hakuri game da abinda suka aikata, sai dai ya yi korafin cewa basu tuntube shi kai tsaye domin neman afuwar shi ba, inda yace da bai duba shafin ba ai ba zai ma san sun bada hakurin ba.

Jariri Hudson dai an haife shi kusan watanni biyu da suka gabata, ya na kuma fama da lalura a zuciyarsa wanda hakan ya sa ake bukatar yi masa dashen sabuwar Zuciya.

'' Wannan dalili ne ya sa na bada wasu kudade domin bude shafi na musammman akan neman taimakon jama'a, ka na na wallafa hotunansa da bayanin yadda lalurar tasa ta ke''. Mahaifin jaririn Mr Kevin ya kara da cewa.