Kerry ya ziyarci Bagadaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Kerry da Haidar al-Abadi

Sakataren wajen Amurka John Kerry, ya gana da sabon Firayi Ministan Iraki Haidar al-Abadi, a Bagadaza babban birnin kasar.

Mutanen biyu sun tattauna kan yunkurin da kasashen duniya ke yi domin samun goyon baya domin a yaki kungiyar IS wacce ke rike da sassa da dama a kasashen Iraki da Syria.

Mr Kerry ya ce ya samu kwarin gwiwa saboda tsare-tsaren da Mr Abadi ya fito da su na yin garambawul a rundunar sojin kasar.

A waje daya kuma akalla mutane bakwai ne suka mutu sakamakon tashin bama-bamai biyu a gabashin birnin na Bagadaza.

Fiye da mutane ashirin ne kuma suka samu raunka.

Bama-baman biyu sun tashi ne a lokaci guda a yankin da ake kira 'New Baghdad', kusa da wata kasuwa.