MNLA ta bude ofis a Holland

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jama'a a Mali sun maida martani a fusace game da labarin cewa 'yan-awaren arewacin kasar sun bude ofishin jakadanci a kasar Holland.

Wani kakakinsu ya ce sun bude ofishin ne a garin Utrecht.

Kasashen duniya di ba su amince da Kungiyar ba.

Ya zuw yanzu dai kasar ta Mali bata ce komai ba akan bude ofishin.

Gwamnatin Holland ta ce 'yan tawayen suna da ikon fadin albarkacin baki don haka baza su na 'yan MNLA din bude ofis a kasar ta ba.

Yanzu haka dai ana cigaba da tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar ta Mali da 'yan tawayen a kasar Algeria don warware matsalar.