Al'ummar Michika na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumar NEMA na kokarin baiwa 'yan gudun hijira taimako

Rahotanni daga garin Michika, wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka kame a jihar Adamawa na cewar ana ci gaba da fafatawa tsakanin mayakan kungiyar da kuma sojojin saman Nigeria.

Sojojin Nigeria na luguden wuta a kan garin na Michika, a kokarin da suke yi na fafarar 'yan kungiyar Boko Haram, inda mazauna garin da yawa ke tserewa

A bangare guda kuma, mutane na ci gaba da yin kaura daga garin Mubi mai makwabtaka da Michika saboda fargabar kada 'yan kungiyar boko haram din su kai musu hari.

Bayanai sun ce mayakan Boko Haram har yanzu suna ci gaba da watayawa a wasu yankuna na garin, inda suke yawo a kan babura da motoci.

A halin yanzu kuma gwamnatin jihar Borno ta aika kayan agaji ga al'ummar garin Gamboru, wadanda ke zaman gudun hijira a Fotokol da ke Jumhuriyar Kamaru.

Akasarin kayan agajin ya kunshi buhunan shinkafa da sauran kayan masurufi.

Sai dai wasu daga cikin 'yan gudun-hijirar na kokawa game da yadda ake rabon kayan.