Tsofaffin sojoji na zanga-zanga a Nigeria

Image caption Ba wannan ne karon farko da tsofaffin sojoji masu karbar fansho ke zanga-zanga a kasar ba

Wasu tsofaffin sojoji na yin zanga-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya bisa rashin biyansu hakkokinsu.

Daruruwan tsofaffin sojojin wadanda suka daura bakaken kyallaye a hannunsu, sun dinga rera wakoki masu sosa rai a yayin zanga-zangar.

Sai dai jami'an tsaro sun dakatar da su a lokacin da suke kokarin kai wa ga fadar shugaban kasa domin mika kokensu.

Zanga-zangar dai na zuwa ne a lokacin da masu sharhi ke ganin matsalar rashin da'a na dada kamari a tsakanin sojojin kasar.

Yayin da wasu ke hasashen cewa akwai rawar da tsofaffin sojojin za su iya takawa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi Najeriyar.

Karin bayani